Wannan kisa dai ya janyo cece kuce tsakanin Al'ummar birnin Kasrin.
Ofishin jikadancin Jamus dake kasar Tunisiya ya bayyana cewa ma'aikatar harakokin kasashen wajen jamus tare da hadin gwuwar Ma'aikatar harakokin kasashen waje na Tunisiya na ci gaba da gudanar da bincike don gane hakikanin wannan lamari.
bayan abkuwar lamarin, Ma'aikatar cikin gida ta kasar Tunisiya ta bayyana cewa jami'an tsaron sunyi halbin ne , yayin da motar ke kudu da ya fice haddi , bayan da jami'an tsaron suka tsayar da motar amma taki tsaya wa.
Har ila yau jami'an tsaron sun bayyana cewa kafin abkuwar lamarin sun samu bayyanan sirri daga tsaunin Sha'anbi na shugowar 'yan ta'adda cikin wannan gari na Kasrin.
Saidai iyalan wadannan 'yan mata sun yi watsi da wannan rahoto inda suka ce bayanai na jami'an tsaro babu kamshin gaskiya a cikinsa. ABNA